Amirul Hajj, Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn el-Kanemi, alhazan na Najeriya suka mikawa korafe-korafen
WASHINGTON, DC —
Shugaban tawagar gwamnatin tarayyar Najeriya a aikin Hajjin bana, mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Ibn el-Kanemi ya ce ya samu korafe-korafe da dama daga alhazan Najeriya a lokacin da ya ziyarci masaukan su a Makka. A taron manema labaran da mai martaba Shehun Bornon ya kira a birnin Jeddah, ya fada cewa korafe-korafen suna da matukar mahimmanci kuma za su sanya su a cikin rahoton da za su mikawa gwamnatin Najeriya idan sun koma gida. Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari na cikin manema labaran da Shehun Borno ya yiwa bayani a birnin Jeddah:
Your browser doesn’t support HTML5