Shehun, wanda ke rangadin wuraren tashin Alhazan shiyyoyi da dama, ya gargadi mata maniyyata da su tabbatar sun tafi Saudiyya ne da muharraminsu. Ya ce duk wadda ta je Saudiyya ba tare da muharrami ba za a maido da ita. Sarkin ya kuma shawarci mata masu ciki cewa su jinkirta aikin hajjinsu har sai lokacin da su ka haihu kuma su ke da karfin yin mawuyacin aiki irin na Hajji. Ya ce duk wadda ta haihu a can za ta shiga mawuyacin hali kuma ta jawo ma hukumomin da abin ya shafa matsala.
Wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhekaya, wanda ya aiko da rahoton, ya ruwaito Amirul Hajj din na cewa jirgin da zai fara maido da Alhazai zai bar Saudiyya ran 28 ga watan Oktoba; yayin da jirgi na karshe zai bar kasa mai tsarkin ran 18 ga watan Nuwamba. Mai Martaban ya kara jaddada ma maniyyata cewa jirgin sama fa baya jiran kowa. Don haka ranar tashi a shirya da wuri. Ya kuma shawarci maniyyata da cewa su yi hankali da kudin guzurinsu tun daga gida Nijeriya da kuma can Saudiyya.