SOKOTO, NIGERIA - Kwanaki kadan suka rage daliban jami'o'in Najeriya su cika watanni bakwai cikin asarar rasa karatu, saboda rashin sasantawa tsakanin kungiyar malaman jami'o'i da gwamnatin kasar, abin da iyaye suka jima suna juyayi tare da yin kira ga malaman da gwamnati da su nemi hanyar sasanta.
A hakan da ake malaman jami'o'in dake mallakar gwamnatocin jihohi suna yajin aikin duk da yake suna karbar albashinsu, abin da ya sa wasu gwamnoni ke ganin ya kamata su sake tunani su daina ci da gumin gwamnati da dalibai da sunan biyayya ko goyon bayan uwar kungiya, a cewar gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a can baya.
“Koda yaushe muna biyan su albashin su, kuma sun kaurace wa aikinsu, suna cin albashi kuma suna goyon bayan wasu, ya kamata su goyi bayan yaranmu ta hanyar sake bude jami'a domin yaranmu su koma ga karatunsu, ba shi yuwa ku yi ta goyon bayan wasu, kan abin bai shafe ku ba, kuna ta goyon bayan uwar kungiyar kuna cutar da dalibanku”.
Ga alama dai wannan kiran bai shiga kunnuwan kungiyar ba, sai uwar kungiyar ma ta kara tsawaita yajin aikin, hakan bai rasa nasaba da shigowar majalisar dokokin Jihar Sakkwato inda ta kafa kwamiti na musamman ya gana da wakilan kungiyar a matakin jiha.
Bayanai dai na nuna cewa a jihar Katsina ma majalisar dokokin jihar ta kira wakilan kungiyar na jami'a mallakar jihar kuma suna kan tattaunawa, yayinda a jihar Kaduna ma tuni gwamna ya umurci malaman da su koma bakin aiki.
Saurari rahoton Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5