Barrister Modibo Zakari y ace a tsarin Nigeria jam’iyya c eke tsayar da mutum takara, ke nan babu wanda zai shiga takarar zabe a Nigeria idan shi bad an wata jam’iyya ba ce.
Idan an zabi mutum zuwa majalisa da sunan wata jam’iyya akwai sharuda goma da zai kiyaye domin muddin ya sabawa daya cikinsu , to zaiyi hasarar kujerarsa. Sai dai idan daya daga cikin wasu sharuda uku ya faru ya na iya ci gaba da rike kujerarsa koda ya bar jam’iyyarsa zuwa wata.
Wadannan sharuda ukun su ne, idan jam’iyyarsa ta dare zuwa gida biyu ko kashi kashi, ko kuma hukumar zabe ta soke jam’iyyarsa, ba zai bar kujerarsa ba. Idan jam’iyyarsa ta hade da wasu shi kuma bai gamsu da hadewar bay a na iya komawa wata jam’iyyar ya ci gaba da rike kujerarsa. Amma idan babu daya cikin sharudan nan uku, tabbas ya yi asarar kujerarsa ke nan.
Akan gwamnonin da suka canza sheka irinsu gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom da gwamnan Kwara Abdulfatah da na Sokoto Aminu Tambuwal, Barrister Maodibo Bakari ya ce dokar kasa ba ta ce komi ba saboda da haka suna kan kujerunsu daram. Kazalika dokar ba ta ce komi ba akan shugaban kasa ko mataimakinsa idan sun canza sheka. Babu abun da za’a yi dasu, sai su ci gaba da rike mukamansu. Barrister Bakari y aba da misali da shari’ar Amechi lokacin da yake gwamna.
Dangane da makomar wadanda suka bar APC suka koma PDP, Barrister Zakari ya ce ba rarrabuwa ba ne. Wata sabuwar jam’iyya aka kirkiro mai suna Rapc. Barrister Bakari babu baraka a APC haka kuma babu baraka a PDP saboda haka wadanda suka canza sheka daga jam’iyyun biyu sun yi asarar kujerunsu baisa doka.
A saurari karin bayani a rahoton Nasiru Adamu El Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5