Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dogara Ya Yi Kaura Zuwa PDP


Kakakin majalisar wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya bi sahun shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wajen yin kaura zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Zuwa yanzu dai kakakin bai sanar da ficewa daga APC a hukumance ba ko sanar da majalisar wakilai don ta na hutu zuwa 25 ga watan nan, amma ya yanki takardar neman takarar majalisar wakilai daga Bauchi a karkashin inuwar jam'iyyar ta PDP.

Jam’iyyar a cewar wata majiya, na gagarumin shirin karbar Dogara a lokacin da zai mika takardar takarar da a ke ganin za a tsaida da shi ba hamaiya.

Matakin na Dogara ya kawo karshen tunanin wasu ‘yan majalisar gani-kasheninsa irin su Gudaji Kazaure da ke da yakinin APC za ta ba wa kakakin tikitin tazarce.

Wasu ‘yan siyasar Bauchi na kai kawo a helkwatar APC da bukatar ta sa baki wajen zaben ‘yar tinke a wajen fidda gwani don gudun kar a kara rasa jama’a ko gaza nasara.

Tsohon ministan lafiya Dr.Muhammad Ali Pate na cikin masu son APC ta tsayar da su takarar gwamnan Bauchi, ya yi togaciyar cewa matukar aka kaucewa tsarin nan APC ka iya shan kaye a Bauchi.

Tuni kakakin APC Yekini Nabena ya ce APC ta rabu da kaya, ya na zargin Dogara da zamba cikin aminci.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara Ya Kaura Zuwa PDP 5'24
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG