Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Jam'iyyar APC Na Ci Gaba Da Mai Da Martani


Ya zuwa yanzu dai ‘ya yan jam’iyyar APC mai mulki a Najeriye, na ci gaba bayyana ra’ayin su game da amincewar da jami'iyyar ta yi na zaben 'yar tinke a zaben shugaban kasa.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne kwamitin koli na Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ya amince da amfani da tsarin ‘yar tinke wajen zabar dan takarar shugaban kasa, yayin da kwamitin ya bar kofa a bude game da salon zabar ‘yan takarar a sauran mukamai.

Tun bayan da kwamitin kolin jam'iyyar APC ya zartar da wancan hukuncin ne kwamitocin zartarwa a matakan jihohi ke gudanar da taron masu ruwa da tsaki da nufin yanke hukuncin daya dace kan sigar zaben fitar da gwani.

Ya zuwa yanzu dai kalilan daga cikin jihohin Najeriya ne musamman wadanda jam’iyyar APCn ke mulki suka zabi amfani da tsarin 'yar tinke a zaben fitar da gwani a matakin gwamna da ‘yan Majalisar Dokoki na kasa dana jiha.

Jihar Katsina na cikin jerin jihohin da suka amince da sigar amfani da wakilai wajen zabar ‘yan takara, yayin da jihar Kano ta fada rukunin jihohin da suka zabi tsarin ‘yar tinke domin fitar da na ta ‘yan Takarar.

Domin karin bayani, saurari rahoton Mahmoud Kwari..

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG