Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Tsohon Shugaba Ibrahim Babangida A Siyasar Nigeria


Masu sharhi na cigaba da tofa albarkacin bakin su game da ziyarar da shugaban majalisar dattawa ya kaiwa tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Idan suke cewa ya kamata Majalisa da Bangaren zartawa su gyara zaman doya da manaja da suke yi

Shi dai Alhaji Bashir Hayatu Jantile ya bayyana cewa ya kamata yan Najeriya su san matsayin tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da matsayin da Allah ya bashi. Ya ce kar a manta cewa Ibrahim Babangida dan jam’iyyar PDP ne tun da yana daga cikin waddanda su ka kafata don su karbi mulki a hannun soja. Dalilin hakan ya sa 'yan PDP ke kallon sa a matsayin uba wanda zai ba su shawara kuma da neman amincewarsa.

Alhaji Jantile ya ce bai yi mamakin kalamansa akan Dr. Bukola Sarki ba, saboda idan aka auna abubuwan da ya ke gayawa duk wanda ya kai mishi ziyara dabam dabam ne da abin da ya fadawa Saraki. Shi dai tsohon shugaban kasa Babangida cewa yayi ‘’ ko ba komai zan goyi bayan ka saboda na rama abinda mahaifin ka ya yi min’’. Janar Babangida ya gayawa Saraki cewa mahaifinsa ya goyi bayan sa saboda haka shima zai goyi bayan shi Bukola Sarakin.

A bangaren sa Malam Bashir M Bashir kwararre kan al’amuran yau da kullum da harkokin sardarwa ya ce idan mutane za su dubi tasirin matsayin wasu a siyasance a Najeriya, wanda ya je gun Babangida matukar ya na takara ko yana da ra’ayin tsayawa takarar neman shugaban kasa, ba laifi ba ne, saboda irin tasirin su da ire iren yadda suka taka rawa wajen tantance al’amuran da suka shafi Najeriya baki daya. Ya ce yakamata a gyara zaman doya da manja da ake yi tsakanin Majalisa da bangaren zartarwa ta Najeriya.

Masu Sharhi Sun Bayana Tasirin Tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida A Siysance 3'25
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG