WASHINGTON, D. C. -Biden ya ce akwai “kwakkwarar hujjar” da za’a iya cewa Firaiminista Benjamin Netanyahu ya jawon rikicin ne don ya samu ceton kan sa a siyasance.
Yayin da yakin ke dab da cika watanni takwas, shugaban na Isira’ilar ya na fuskantar bukatu masu cin karo da juna, daga Biden da sauran shugabannin duniya, don kawo karshen rikicin, yayin da ‘yan majalisa masu ra’ayin rikau a majalisar dokokin Isira’ila suka ce za su yi watsi da goyon bayan Netanyahu tare da karfafa gwamnatinsa idan ya amince da tsagaita wuta, ba tare da kawar da ragowar ikon Hamas a Gaza ba.
Hamas dai ta fada jiya Talata cewa, ba za ta iya amincewa da duk wata yarjejeniya ba, sai dai idan Isira’ila ta fito fili ta bayyana tsagaita wuta na dindindin da kuma janye sojojinta gaba daya daga Gaza. Netanyahu kuwa ya sha cewa sojojin Isira’ila ba za su bar Gaza ba, ba tare da kawar da dukkan burbushin Hamas daga yankin ba.