Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Rafah Mummunan Kuskure Ne - Netanyahu


Netanyahu
Netanyahu

Firaiminista Benjamin Netanyahu ya fada ranar Litinin cewa an yi "kuskure mai ban tausayi" a harin da Isra'ila ta kai birnin Rafah da ke kudancin Gaza, wanda ya kona wani sansanin da ke dauke da Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, kuma a cewar jami'an yankin, akalla mutum 45 suka rasa rayukansu.

WASHINGTON, D. C. - Wannan harin dai ya kara kakkausar sukar da kasashen duniya ke yi kan Isra'ila, a yakin da take yi da kungiyar Hamas, inda hatta kawayenta na kut-da-kut suka nuna bacin ransu kan mutuwar fararen hula.

Isra'ila ta dage cewa tana bin dokokin kasa da kasa duk da cewa tana fuskantar shari'a a manyan kotunan duniya, wanda a makon da ya gabata daya daga cikinsu ya bukaci dakatar da kai farmakin a Rafah.

Netanyahu bai yi karin bayani kan ko wane irin kuskuren ne ba.

Da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai wani madaidaicin hari ta sama kan wani yanki na Hamas, inda ta kashe wasu manyan mayakan sa kai guda biyu.

Yayin da ake samun cikakken bayani game da harin da kuma tashin wutar, rundunar sojin ta ce ta bude bincike kan mutuwar fararen hula.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG