Akwai Bukatar Kara Farashin Man-Fetur A Najeriya-Bankin Duniya

Bankin Duniya

Bankin Duniya ya ce bai kamata Najeriya tana sayar da litar man-fetur a farashin Naira 650 ba, duba da yadda musayar kudaden kasashen ketare suke a yanzu.

Bankin Duniyar, yace kamata yayi a sayar da litar man-fetur Naira 750 a Najeriya domin ya tafi daidai da abinda ke kasa a zahiri. Bankin na mai ra'ayin cewa, har yanzu gwamnatin Najeriya tana biyan kudin tallafin Man-fetur, idan aka yi la'akari da yadda farashin yake a yanzu.

Bankin na Duniya ta bakin wakilinta dake kula da fannin tattalin arziki a Najeriya Alex Sienaert, ya ce " kamata yayi gwamnatin Najeriya ta sayar da litar man-fetur akan farashin Naira 750, saboda ya kasance matsaya daya da yadda musayar kudaden kasashen ketare yake a kasar"

Alex Sienaert, ya bayyana hakane a Abuja, lokacin da yake gabatar da jawabin manufofin kasar, ta (farfadowa, sabuwar manufa da kuma sakamako).

Mista Sienaert, ya kara da cewa "idan muka kiyasta yadda farashin litar man-fetur yake a yanzu, da kuma yadda farashin canjin kudaden ketare suke, zaka ga cewa gwamnatin kasar na biyan kudin tallafin man-fetur, domin Najeriya na amfani ne da kudaden kasashen ketare wajen shigowa da Man-fetur a kasar, dan haka kamata yayi, gwamnatin kasar ta sayar litar man-fetur akan farashin Naira 750".

Sai dai masana na ganin wannan shawara ta Bankin Duniya ka iya mayar da hannun agogo baya, kuma hakan zai taimaka wajen kara hauhauwar farashin kayakin a kasar, da kuma kassara tattalin arzikin kasar, da zai haifar da halin kunci duba da yadda rayuwa ke da matukar tsada yanzu a kasar, a cewar Aliyu Usman Jibo, masanin tattalin arziki kuma Malami a makarantar koyar da Malamai dake jihar Jigawa.

Da yake tsokaci kan wannan shawarar a hirarsa da Muryar Amurka, Bashir Salisu Tahir, shugaban dillalan Man-fetur ta IPMAN reshen Arewa maso yammacin Najeriya, ya ce "ba Bankin Duniya ba ne ya kamata ya kayyade farashin man-fetur a Najeriya, kuma wannan karin da Bankin Duniya yayi ikirari, kassara kasuwar man-fetur kawai zayyi a Najeriya".

Yanzu dai hankulan 'yan kasar ya karkata ne ga gwamnatin tarayya, ko zata yi amfani da wannan shawara ta Bankin Duniya ko kuma zatayi la'akari da halin kunci da yan kasar suke ciki.

Saurari rahoton Rukaiya Basha:

Your browser doesn’t support HTML5

Bankin Duniya Ya Ce Gwamnatin Najeriya Ta Kara Farashin Man-Fetur A Kasar.