Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne aka fara sauke gangar mai miliyan daya daga rijiyar mai na Agbami da ke gabar tekun Neja-Delta a wani jirgin ruwa a matatar da ke yankin Free Zone na Lekki da ke gabashin Legas, cibiyar tattalin arziki.
"Wannan wani muhimmin ci gaba ne," in ji Aliko Dangote, wanda ya kafa matatar man Dangote a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, inda ya kara da cewa "babban mataki na gaba shi ne mu kai kayayyakin mu zuwa kasuwannin Najeriya".
Matatar man da ta shirya fara aiki a “karshen watan Yuli, zuwa farkon watan Agusta”, ana sa ran zata tace man da zai taimaka wa Najeriya ta kawo karshen karancin man fetur da ake fama da shi akai-akai, da kuma kara ingancin man da ke zagayawa a kasuwanni.
Najeriya mai yawan al'umma miliyan 215, na daya daga cikin manyan masu arzikin man fetur a nahiyar Afirka, amma kusan tana shigo da dukkanin man da take amfani da shi daga kasashen waje ne sakamakon gazawar matatun man kasar, da ke haddasa karancin man fetur da ya addabi rayuwar al'umma ta yau da kullum.
Aikin da aka kaddamar a shekarar 2013, na dala biliyan 18.5 tare da masana'antu wanda ya ninka kudinsa na fari, shine "matar mai mafi girman a duniya dake ayyuka da dama wuri daya", a cewar Rukunin kamfanin Dangote, kuma idan zata aiki da dukkan karfinta, zata tace mai fiye da duk wata matata a nahiyar Afirka.
Ana sa ran matar zata tace ganga 350,000 a kowace rana da farko, kana adadin zai karu zuwa 650,000 idan ta fara aiki cikakke, sannan kuma zata a samar da dizal, man jirgin ssama, man motoci, da kuma iskar gas.
Ana kuma shirin sake kai ganga miliyan 5 a cikin makonni masu zuwa.
~Africanews~
Dandalin Mu Tattauna