Rade-radin da ake yi cewa, Najeriya ta sayar da danyen man fetur na tsawon shekaru takwas nan gaba, na karuwa a tsakan kanin al’ummar kasar da hakan ke nuna halin rashin tabbas na tattalin arzikin kasar. Gwamnatin kasar da shugaba Tinubu ke jagoran ta ba ta tabbatar ko musanta labarin ba.
Neman izinin ciwo bashin dalar Amurka biliyan 8.69 da Fam miliyan 100 ya kara nuna bukatar kudi da gwamnatin ke da ita na neman hanyar ciwo bashi, lamarin da ya sake tado batun sayar da danyen man bisa bashi, duk da dimbin bashin da gwamnatin Tinubun ta gada daga gwamnatin da ta shude, ta Muhammadu Buhari.
Masanin kididdiga, kuma wanda ya tallafa wajen lissafa kuri'un shugaba Muhammadu Buhari a dakin baiyana sakamakon zaben shekarar 2015, Farfesa Sadik Umar Gombe ya ce, labari mai inganci ya tabbatar da dogaro kan kudin Mai ga Najeriya a yanzu lissafin dawakin rano ne kawai.
Sahihin labari na maganar cewa gwamnatin da ta shude ta Muhammadu Buhari ta saida danyen mai na kwatankwacin shekaru 6, ga kuma na wannan gwamnatin mai watanni kadan, idan ya sayar da na shekaru 3, kenan shekaru 9 za ayi nan gaba, balle kuma ace wannan gwamnatin har za ta yi shekaru 8 masu zuwa, kenan sai ta yi shekara 8 ba ta gama biyan man da a ka karba ba. Shekaru 9 nan gaba Kusan duk abun da a ka sayar yanzu bashi za a rika biya da kudin.
A yayin wata hira ta musamman da mai baiwa shugaba Tinubu shawara ta musamman kan al’amurran siyasa da aiyuka na musamman Ibrahim Kabir Masari, ya ki ya tabbatar ko ya karya ta labarin ba, ya ce, tone-tone a yanayin da a ke ciki ba zai taimakawa kasar ba.
Tashin farashin dala akan Naira da tashin farashin kayayyaki da ya kai fiye da kashi 27 cikin 100 a mizanin ma’aunin farashi, ya sa talakawa, har ma da matsakaitan masu samu na ji a jika, inda ala tilas mutane kan sauya tsarin rayuwar su inda da dama ake ci hannu baka hannu kwarya.
Dandalin Mu Tattauna