Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Direbobin Tankar Mai A Najeriya Na Barazanar Fice wa Daga NUPENG


Tankokin dakon mai (Hoto: Facebook/NUPENG)
Tankokin dakon mai (Hoto: Facebook/NUPENG)

Kungiyar ta NUPENG ta yi watsi da zarge-zargen kungiyar direbobin tankar man.

Kungiyar direbobin tankar mai a Najeriya PTD na barazanar ficewa daga uwar kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta NUPENG.

Direbobin tankar na so ne shugaban kungiyar ta NUPENG Williams Akporeha da Babban Sakatarenta, Afolabi Olawale su yi murabus daga mukamansu.

Cikin wata sanarwa da kungiyar direbobin ta fitar dauke da sa hannun daya daga cikin jami’inta, Gbenga Olawale, a ranar Lahadi, direbobin sun yi barazana shiga yajin aikin gama-gari inda har ba a biya musu bukatunsu ba.

A cewar sanarwar, Williams da Akporeha ba su da kwarewar da za su jagoranci kungiyar, saboda haka su yi murabus.

Sanarwar ta kuma zargi Williams da yunkurin tsayawa takarar shugban kungiyar ta NUPENG, wani abu da ya ce ya sabawa dokokin kungiyarsu PTD.

Kungiyar ta NUPENG ta yi watsi da zarge-zargen kungiyar direbobin tankar man.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG