Akalla Falasdinawa 90 Suka Mutu A Wani Harin Da Isira'ila Ta Kai Kan Makaranta

Wani Yaro Da Ke Zaune Kan Baraguzan ginin Makaranta A Nuseirat Da Ke Tsakiyar Zirin Gaza, July 9, 2024.

Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta fada a yau Asabar cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon harin sama na baya bayan nan da Isira’ila ta kai kan wata makaranta da Falasdinawa ke zaune wadanda suka rasa matsugununsu ya haura 90.

Yayin da rundunar sojin Isira’ila ta ce ta kai hari kan wata cibiyar bayar da umarni ta mayakan.

Kafmanin dillacin labaran AFP ya kasa tantance adadin wadanda suka mutu, wanda idan har aka tabbatar da hakan zai zama daya daga cikin hari mafi girma guda daya da aka kai cikin tsawon watanni 10 na yaki a Gaza tsakanin Isira’ila da Hamas.

Kakakin hukumar Mahmud Bassal ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP cewa, adadin wadanda suka mutu ya kai 90 zuwa 100, kuma akwai wasu da dama da suka samu rauni.

Rokoki uku na Isira’ila suka afkawa makarantar da ke dauke da Falasdinawa da suka rasa matsugunansu.”

Ofishin yada labaran gwamnati a Gaza da ke karkashin mulkin Hamas ya ce harin ya yi sanadin kashe mutane fiye da 100.

Yayin da akasarin mutanen Gaza miliyan 2.4 suka rasa matsugunansu a yakin da Hamas ta fara kai hari a kudancin Isira’ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara, lamarin da yasa da dama daga cikinsu suka nemi mafaka a gine-ginen makarantu.

Harin na ranar Asabar ya kawo akalla adadin makarantu 14 da aka kai wa hari a Gaza tun ranar 6 ga watan Yuli, inda aka kashe fiye da mutane 280, a cewar wasu alkaluma kamfanin dillancin labarai na AFP na adadin da jami’ai a yankin suka bayar a baya.

AFP