Rediyon sojan ya ce ba a iya gane ko an kashe shugaban na Hamas Mohammed Deif ba. Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce tana tantance rahoton.
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fada a wata sanarwa cewa asibitin Nasser dake Khan Younis ya amshi gawarwaki 20 da mutane 90 da suka jikata. Sanarwar bata yi karin bayani a kan adadin wadanda lamarin ya rutsa da su da aka kaisu wasu asibitotcin ba.
Kafar labaran Hamas ta ce an kashe akalla mutane 100 kana aka jikata wasu da dama ciki har da ma’aikatan agajin gaggawa.
Wani babban jami’in Hamas bai tabbatar da ko Deif na nan a wurin ba.
"Zargin Isra’ila na rashin hankali ne kuma har suna so su kare wannan mummunan barna da suka yi. Wadanda suka mutun dukkansu fararen hula ne kuma abin da ya faru wani mummunan salon yakin kare dangi ne, wanda Amurka ke marawa baya kuma duniya ta yi shuru tana kallo," in ji Abu Zuhri yana fadawa kanfanin dillancin labaran Reuters.
Wani harin da Hamas ta jagoranta ya kashe mutane 1,200 kana suka suka yi garkuwa da wasu 250 a wani samame da mayakan suka kai a iyakar kudancin Isra’ila a watan Oktoba, a cewar lissafin Isra’ila.
Isra’ila ta mayar da martani da karfin soja a Gaza inda ta kashe sama da Falasdinawa 38,000, a cewar hukumomin lafiya a birnin na Gaza.
Dandalin Mu Tattauna