Akalla 50 Suka Jikkata Bayan Da Wani Jirgin LATAM Mai Zuwa Auckland Ya Samu Tangardar Na’ura

Latam Airlines, Chile

Akalla mutane 50 ne suka jikkata a ranar Litinin, akasarinsu da kananan raunuka, bayan da kamfanin jirgin LATAM ya shaidawa jaridar New Zealand Herald cewa ‘tangardar na'ura’ ta sabbaba wani ‘kwakkwaran motsi’ a tafiyar wani jirgin sama daya tashi daga birnin Sydney zuwa Auckland a kasar Australia.

WASHINGTON, D. C. - Jirgin LATAM Airlines LA800, Boeing 787-9 Dreamliner, ya sauka a filin jirgin saman Auckland kamar yadda aka shirya a ranar Litinin da yamma, a cewar FlightAware. Jirgin ya saba tsayawa a Auckland akan hanyarsa ta zuwa Santiago, Chile ne.

Wani jirgin LATAM Airlines Boeing 787 na shirin sauka a kasar Lisbon - Yuli 5, 2023.

Wani mai magana da yawun kamfanin jirgin na Kudancin Amurka wato American Airline ya shaidawa jaridar Herald cewa an samu "matsalar fasaha" a cikin jirgin da ya shafi wasu ma'aikata da fasinjoji, ba tare da bayar da karin bayani ba.

Motar daukar marasa lafiya ta Hato Hone St. John ta yi wa mutane kusan 50 jinya a filin jirgin, kamar yadda mai magana da yawun ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Majinyaci ɗaya yana cikin wani mummunan yanayi, kuma sauran sun sami raunuka masu sauƙi zuwa matsakaici, in ji su.

Wani jirgin LATAM Airlines a Portugal

Boeing da LATAM dai ba su amsa tambayoyi daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ba game da musabbabin lamarin da kuma yanayin lamarin.

-Reuters