Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Herbert Wigwe Mutum Ne Mai Natsuwa, Fara’a Da Tsabta – Abokan Karatunsa


Herbert Wigwe
Herbert Wigwe

Ana ci gaba da alhinin hadarin jirgin saman mai saukan angulu da ya yi sanadin salwantar rayukan mutane akalla shida ciki har da Shugaban bankin Access, Herbert Wigwe da matarsa da dansa.

Wasu da ga cikin abokan karatun Mr Herbert dake Sakkwato sun yi tsokaci a kan zamantakewa da suka yi da shi, duk da yake ya fito daga yankin kudancin Najeriya.

Daya daga cikin abokan karatun Mr Herbert, wanda dan asalin Sakkwato ne, Mu'azu Ahmadu Suka ya yi tsokaci a kan haduwar su a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwato, yace aji daya kuma dakin kwanan dalibai daya suke, sun shiga kwalejin a 1976 zuwa 1979 sai marigayin ya canja makaranta.

A lokacin zaman su yace Mr Herbert mutum ne mai natsuwa mai fara'a kuma mai tsabta, kuma tsawon lokaci bai canja kamanunsa ba.

Wannan lamarin shi ya kara nunawa a fili irin muhimmancin da ke ga wadannan makarantu na hadin kan 'yan Najeriya.

Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar Tsofaffin Dalibai ta Kwallejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwato, Hassan Muhammad Maccido, yace samuwar wadannan makarantu ya kawo fahimtar juna tsakanin 'yan kudu da 'yan arewa ta yadda duk inda mutum ya je zai ji tamkar yana gida.

Wasu daga cikin abokan karatun shuagaban bankin na Access sun bayar da kyakkyawar shaida a kan rayuwar sa.

A halin da ake ciki dai an bude rijistar yin ta'aziyar marigayin a bankunan Access inda jama'a ke saka hannu suna ta'aziyar.

Herbert Wigwe da matarsa da dansa tare da wasu mutane uku sun rasu ne a cewar wata jaridar US TODAY ranar Juma'a 9 ga watan Fabrairu 2024 a wani hadarin jirgin sama mai saukan angulu a yankin hamadar kudancin California.

Tuni dai jama'a suka fara ta'aziyar rashin, ciki har da Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu, kamar yadda jaridar ta wallafa.

A saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

Herbert Wigwe Mutum Ne Mai Natsuwa, Fara’a Da Tsabta – Abokan Karatunsa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG