Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Fasinja Ya Yi Hatsari A Mogadishu


FILE - Airplanes are parked at Aden Adde International Airport in Mogadishu, Somalia, on Feb. 13, 2022.
FILE - Airplanes are parked at Aden Adde International Airport in Mogadishu, Somalia, on Feb. 13, 2022.

Jirgin fasinja na cikin gida ya yi hatsari a filin jirgin saman Mogadishu.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Somaliya ta fada a wata sanarwa cewa dukkan fasinjoji 30 da ma'aikatan jirgin hudu sun tsira.

Jirgin saman samfurin E-120, mallakar kamfanin jiragen sama na Halla Airlines ya taso ne daga birnin Garoowe na yankin Puntland na Somaliya zuwa filin jirgin saman Aden Adde na Mogadishu.

"Babu rasa rayuwa a hadarin sai dai kananan raunuka," in ji SCAA a cikin wata takaitacciyar sanarwa. "Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Somalia na son sake tabbatar da cewa za'a fitar da rahoton farko da zarar an kammala binciken da ake yi a yanzu."

Hotunan da aka yadda ta talabijin ya nuna jirgin ya kauce daga titin tashi da saukar jirage ne nan take bayan ya sauka.

Matukin jirgin bai bayar da rahoton wata matsala ba ga hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama kafin faruwar lamarin.

Ismail Mohamud na kamfanin jiragen sama na Halla ya shaidawa Muryar Amurka cewa daga baya za'a fitar da rahoton sakamakon binciken.

Alamu na farko sun nuna cewa mai yiwuwa kuskuren matukin jirgin ne ya haddasa hadarin, a cewar wani jami'in Somaliya da ya bukaci a sakaye sunansa.

Ya kara da cewa "Za a tabbatar da gaskiyar lamarin da zarar an yi nazarin na'urar nada murya da akwatin bayyana bincike na cikin jirgi."

Hukumomin filin tashi da saukar jiragen sama na Somalia sun inganta ayuka a cikin 'yan shekarun nan, inda suka sake karbe ikon zirga-zirgar jiragen sama daga Majalisar Dinkin Duniya. A farkon wannan shekarar, Somaliya ta dawo da matsayinta na ajin farko daga kungiyar sufurin jiragen sama ta kasa da kasa.

Jirage sama da 150 na cikin gida da na ketare ne ke amfani da filin tashi da saukar jiragen sama na Mogadishu a kullum, a cewar hukumar kula da filayen jiragen sama. Manyan kamfanonin jiragen sama na kasa-da-kasa da ke amfani da filin jirgin sun hada da Turkish Airlines, Qatar Airways da Ethiopian Airlines.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG