A jamhuriyar nijer kungiyar lauyoyi ta ja hankulan rukunonin al’umar kasar da su gujewa furta kalaman dake da nasaba da dalilan kabilanci ko bangaranci sakamakon la’akari da yadda kalaman batanci suka mamaye mahawarori a ‘yan kwanakin nan a tsakanin magoya bayan bangarorin siyasar nijer a shafikan sada zumunta.
Me Idrisa Cirnaka, jigon kungiyar, shi ne ya karanto sanarwar kungiyar lauyoyin ( barreau de l’ordre des avocats) . Kafafen sada zumunta da suka hada da FaceBook da Twitter da Whats’up sun kasance wani fagen cin zarafin juna da ashar kala kala tsakanin magoya bayan ‘yan siyasa saboda haka kungiyar lauyoyi ta yunkuro.
Shi ma wani mamba a kungiyar mai suna Me Nasara Umaru ya daddada bukatar da ke akwai ta kai zuciya nesa da kuma aiki da hankali tsakanin jama'a masu mabanbantan ra'ayoyi.
Kungiyar ta lauyoyi ta ce nauyi ya rataya a wuyan shuwagabannin rukunonin al’uma daban daban na kasar da su kawo karshen wannan sabon al’amari tun lokaci bai kure ba.
Mummunar muhawarar da aka tafka a baya bayan nan tsakanin masu anfani da kafafen sada zumunta ta sa hukumomin Nijarr toshe wadannan kafafe a karshen makon jiya .Dokokin Jamhuriyar Nijar sun tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda ke furta kalaman kabilanci ko bangaranci a fili.
Your browser doesn’t support HTML5