Hukumar Samar da Abinci Ta Majalisar Dinkin Duniya, tare da hadin gwiwar kungiyoyin mazauna karkara, ta shirya wani taro a Janhuriyar Nijer wanda yake duba ire-iren matsalolin da mazauna karkara ke fuskanta tare da nazarin hanyoyin magance su, a cewar wakilinmu Yusuf Abdoulaye.
Daya daga cikin wadanda su ka shirya taron mai suna Abdulkarim Mammalo, ya bayyana ma Yusuf cewa sun gayyaci manoma da makiyaya da mata da maza da mataza da sauransu, don ganin yadda za a tabbatar da zaman lafiya tsakanin dukkannin rukunonin da ke karkara- ta yadda kowa zai yi sana’arsa ba tare da wata matsala ko tsangwama ba.
Alhaji Abdulkarin y ace kasar na fuskatar talauci saboda rikice-rikice da rashin daidaito da adalci. Hadda rashin bai wa mata kasonsu na gado al’amari ne mai tsanani a karkara.
Shi kuma daya daga cikin makiyayan da ke halartar taron mai suna Abdou Nino y ace sana’ar kiwo na fuskantar barazana sosai a Janhuriyar Nijar saboda yawan cinye labi da burtaloli da manoma ke yi. Don haka ya bukaci da a kawo karshen wannan al’amarin.
Ga Yusuf Abdoulaye da cikakken rahoton: