AFCON: Angola Ta Kada Namibia Gida

Dan wsan Angola Mabululu yana murnar zura kwallo a ragar Namibia a gasar kofin AFCON da ake yi a Ivory Coast (Photo by KENZO TRIBOUILLARD /

Mabululu ya kafa tarihi a Angola na dan wasan kasar na farko da ya taba cin kwallaye uku a gasar kofin nahiyar Afirka.

Angola ta fitar da Namibia a gasar kofin nahiyar Afrika ta AFCON da ake yi a Ivory Coast bayan da ta doke ta da ci 3-0.

Dan wasan Angola, Gelson Dala ne ya zura kwallaye - biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Da aka dawo kuma Agostinho Mabululu ya zura kwallo ta uku.

Wasan ya yi zafin da sai da alkalin wasa ya ba kowane bangaren jan kati - abin da ya sa dukkan su suka buga wasan da 'yan kwallo goma-goma.

Mabululu ya kafa tarihi a Angola na zama dan wasan kasar na farko da ya taba cin kwallaye uku a gasar kofin nahiyar Afirka.

Yanzu Angola ta shiga zagayen Quarter-Finals a gasar.

Wannan sakamakon wasa na nufin Angola za ta kara da wanda ya yi nasara a karawa tsakanin Najeriya da Kamaru.