Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Algeria Da Burkina Faso Sun Yi Kunnen Doki


Wasan Algeria da Burkina Faso
Wasan Algeria da Burkina Faso

Algeria da Burkina Faso sun tashi da ci 2-2 a wasan da suka kara a Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta AFCON da ake yi a Ivory Coast.

Dan wasan Burkina Faso Mohamed Konate ne ya fara zura kwallo a ragar Algeria gab da ana shirin tafiya hutun rabin lokaci.

Sai dai bayan an dawo dga hutun rabin lokaci, dan wasan Algeria Baghdad Bounedjah ya farke kwallon a minti na 51.

A cikin minti na 70 ne kuma Burkina Faso ta sake samun wata damar inda dan wasanta Bertrand Traore ya zura kwallo ta biyu a ragar Algeria ta hanyar bugun fenariti.

Sai dai murna ta koma ciki ga ‘yan wasan Burkina Faso bayan da Bounedjah ya zura kwallo ta biyu a ragarsu.

Hakan ya karawa Algeria kwarin gwiwar samun zuwa zagayen ‘yan 16.

Yanzu dai Burkina Faso ce a saman teburin rukunin D da maki hudu, Algeria na biye da ita da maki biyu.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG