Gwamna Nyako Yayi Allah Wadai Da Shirin Kara Wa'adin Dokar Ta Baci a Jihar

'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya su na sintiri

Adamawa ta bayyana takaicin kara wa'adin dokar ta baci da gwanatin tarayya take shirin yi.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta mika kuduri ga majalisun dokokin kasa da nufin kara wa'adin dokar ta baci, da shugaban kasa Dr. Goodluck Rebele Jonathan ya kafa kan jihohi uku Borno, Yobe, da Adamawa wadnda suke arewa maso gabashin kasar.

Da yake magana kan wannan sabon kuduri, Gwamna Murtala Nyako ta bakin darektan yada labaransa Mallam Ahmed Sajo yace saka jihar cikin jerin jihohin nan uku tunda farko ma bai dace ba, domin babu wani tashin hankali da ake yi ajihar. Mallam Ahmed Sajo yace bayanda aka kafa dokar jihar tayi bakin kokarinta wajen gani babu dan jihar daya da aka kashe tun kafa dokar, saboda irin hadin kai da gwamnati da al'umar jihar suka baiwa wannan shiri. Har zuwa yanzu babu dan jihar mutum daya da aka kama kan zargin ta'addanci. saboda haka idan dai ba akawai wata manufa ba, babu dalilin sake saka Adamawa a cikin jerin jihohin da za'a kara karfafa wannan doka.

Daga nan Ahmed Sajo yayi kira ga wakilan majalisun dokokin tarayya cewa idan shugaban kasa ba zai yiwa jihar Adamawa adalci ba, to tilas ne su su yiwa jihar adalci. Ya yi kira garesu da su ziyaci jihar Adamawa domin tantance halinda ake ciki dangane zaman lafiya da ake da ita a jihar.

Gwamnatin wacce ta dauki wannan mataki watanni shida da suka wuce da niyyar yaki da tashe tashen hankulan da mayakan sakai da ake kira Boko Haram suke tayarwa, musamman a jihohin Borno da Yobe ta sa gwamnatin katse hanyoyin sadarwa cikin wadan nan jihohi na watanni. Kodashike har yanzu wannan doka tana aiki a jihar Barno.

Your browser doesn’t support HTML5

Dokar Ta Baci A Adamawa