Sheikh Abdullahi Bala Lau shugaban kungiyar IZALA ta kasa ya bayyana mahimmancin adduo'in.
Yace yaki da tabarbarewar tsaro da durkushewar tattalin arziki ba aikin mutum daya ba ne. Wadanda aka zaba kuma ba mala'iku ba ne. Ba zasu iya kawo gyara ba cikin kwana biyu ko uku sai an hadu dasu sun yi iyakar nasu kokari kana jama'a na yin addu'a ana rokon Allah.
Yace wannan wata na azumin Ramadan lokaci ne da ya kamata a yi irin wadannan addu'o'in. Allah yana karbar addu'o'i cikin wannan watan saboda haka a mika masa halin da kasar ke ciki. A rokeshi ya rikawa shugabannin kasar da halin da al'ummarta ta samu kanta a ciki. A tuba domin Allah ya tausaya, ya kawo karshen tabarbarewar tsaro. Ya kawowa kasar cikakken tsaro.
Azumin bana ya zo ne yayinda 'yan Najeriya ke fama da matsalar tattalin arziki. Lamarin ya sa shugabannin addini na ganin dole ne masu hannu da shuni su taimakawa masu karamin karfi. Sheikh Bala Lau yace yakamata masu hannu da shuni su dauki dukiyarsu su taimakawa talakawa musamman a wannan watan saboda da dimbin albarka. Ya kira su daure su dinga karanta Kur'ani koyaushe.
A wata sabuwa kuma Kiristoci a jihar suna taya Musulmai 'yanuwansu da yin azumi na neman samun hadin kai da cigaban kasa. David Maloma yana taya musulmi yin azumi. Yace musulmai na kawo masu kayan bude baki. Yace ko dansa mai shekaru goma sha bakwai shi ma yana yin azumi da sunan yiwa Najeriya.
David Maloma ya kira 'yan Najeriya da su hada kai. Yace ko barayi ma na hada kai. Sau da yawa idan an kama kungiyar barayi sai a ga akwai musulmai da kiristoci cikinsu.Idan za'a yi yaki ba'a tunawa da addini saidai an zo yin siyasa lokacin ake kawo banbanci.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5