A ranar Litinin jam’iyyar Republican ta fara babban taronta a Milwaukee, babban birnin jihar Winsconsin da ke Amurka.
Taron na wakana ne kwana biyu bayan da ji wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump rauni yayin wani gangamin yakin neman zabe – wani abu da ake kallo a matsayin yunkuri na halaka shi.
Jam’iyyar ta Republican ta jajirce cewa taron zai gudana duk da wannan hari da aka kai kan dan takararta.
A wannan taro ake sa ran za a tabbatarwa da Trump cewa shi ne zai zama dan takarar jam’iyyar.
Babu masaniya kan yadda wani hari zai yi tasiri akan taron, wanda za a kwashe kwanaki hudu ana yi.
Wani abu da aka sani shi ne, yadda jami’an tsaro suka tsaurara matakan tsaro a wajen taron, wanda an saba yin shi cikin yanayi na biki.
Tuni dai dukkan bangarorin siyasar kasar suka yi Allah wadai da wannan mummunan al’amari inda kowa ya yi ta kira da a hada kai.
Sai dai wasu ‘yan Republican suna dora laifi akan Shugaba Joe Biden, suna masu cewa kalaman da yake yi na cewa Trump barazana ce ga tsarin dimokradiyya, su suka haifar da wannan hari.
Wasu daga cikinsu har ila yau, sun nemi masu shigar da kara da a janye duka tuhume-tuhume da ake yi wa Trump, ciki har da wanda aka same shi da laifi.
Yayin da jami’ai , ‘yan siyasa da wasu Amurkawa ke shirin yin jawabi a taron, tambayar it ace, shin da wane irin lafazi za su yi magana – za a yi amfani da kakkausan lafazi ne ko tattausa?
Tun gabanin a kai hari kan Trump a ranar Asabar, mafi aksarin kan ‘yan Republicans a hade yake, inda suka kuduir aniyar sake jaddada hadin kan jam’iyyar a wannan taron.
Sai dai ana ganin hadin kan zai kara fitowa fili inda a ranar Lahadi Trump ya ce “ya fi muhimmanci fiye da kowane lokaci mu hada kanmu, mu nuna asalin halayenmu a matsayin Amurkawa, tare da nuna jajircewa saboda kada mu bari muggan iris u samu nasara.”
Wannan hadin kai da ake gani a yanzu, ya sha banban da wanda aka gani a baya-bayan nan.
A shekarar 2016, karo na farko da aka zabi Trump a matsayin dan takarar jam’iyyar, an samu hatsaniya a ranar farko da aka bude taron daga wakilan da ke adawa da shi.
Bayan da ya kammala wa’adinsa na farko inda a karshe magoya bayansa suka kai hari ginin majalisar dokokin Amurka, farin jinin Trump ya yi kasa sosai a lokacin da ya nuna sha’arwarsa ta sake tsaya a shekarar 2022.
Amma duk da haka, Trump ya kawar da dukkan abokana hamayyarsa a jam’iyyarsa ta Republican ya kama had akan magoy bayansa.
Har yanzu Trump bai bayyana sunan mataimakinsa ba, ana kuma sa ran a ranar Litinin zai sanar.
Daga cikin mutane uku da ake sa ran zai zaba, akwai Sanata J.D. Vance na jihar Ohio, Sanata Marco Rubio na jihar Florida da gwamnan North Dakota Doug Burgum.
Dukkan ‘yan takarar za su yi jawabi ga wakilan ‘yan Republican kamar yadda jadawalin taron ya nuna.
Bisa al’ada, duk wanda Trump ya zaba, zai gabatar da jawabi a daren Laraba.
A cewar gangamin yakin neman zaben Trump, taken wannan taro shi ne “Sake farfado da tattalin arzikin Amurka.