A Yi Gyara A PDP, Ko A Binne Ta - Murtala Nyako

Hotunan Babbban Taron Jam'iyyar PDP a Abuja

Murtala Nyako, daya daga cikin gwamnonin da suke bori ma PDP-Tsohuwa yace zasu ci gaba da fautukar kawo sauyi a jam'iyyar, ko kuma su binne ta
Bangaren jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya da ake kira PDP-Sabuwa, ta ce har yanzu tana nan a kan bakarta ta fafutukar kawo sauyi a cikin jam'iyyar, amma kuma idan har shugaban kasa Goodluck Jonathan, da sauran shugabannin bangaren PDP-Tsohuwa suka ci gaba da yin ko oho da muradun 'ya'yan jam'iyyar, zasu taimaka wajen yin jana'izarta.

Gwamna Murtala Nyako na Jihar Adamawa, daya daga cikin gwamnonin jam'iyyar PDP su 7 da suka kafa bangaren PDP-Sabuwa karkashin jagorancin Kawu Baraje, yace zasu ci gaba da kasancewa cikin PDP domin ganin an samu gyara, kuma idan zata mutu ne, sai dai ta mutu a hannunsu.

Sakataren PDP-Sabuwa a Jihar Adamawa, Mr. P.P. Elisha, yace duk da hukumcin da kotu ta yanke cewa ba ta san wata PDP-Sabuwa ba, su kam yanzu suka fara babu ja da baya, zasu ci gaba da gwagwarmayar neman sauyi.

Shi kuwa Barrister A. T. Shehu, sakataren PDP-Tsohuwa ta Bamanga Tukur a Jihar Adamawa, yace su kam ba su ma san da zaman wata PDP-Sabuwa ba, tun da kotuna ma sun ce a bisa shari'a babu wata PDP-Sabuwa.

Wadannan duk su na zuwa a daidai lokacin da jami'an dake goyon bayan tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar, suke wani taron tsara dabarun yadda gwanin nasu zai doshi zaben 2015 mai zuwa.

Ibrahim Abdulaziz yana tafe da cikakken bayani daga Yola.

Your browser doesn’t support HTML5

Sabuwar PDP Ta Ce Tana Kan Bakarta-Ko A Yi Gyara Ko Su Binne Ta - 2:47