To amma samo rancen ya kai ga sauya kalamu tsakanin gwamnan jihar Murtala Nyako da bangaren PDP na Bamanga Tukur. Wannan batu dai ya kai har wasu 'yan jihar sun garzaya kotu domin kalubalantar rancen. Cikin martanin da shugaban PDP bangaren Bamanga Tukur ya mayar ya ce da wata manufa aka ciwo bashin. A jawabinsa sakataren jam'iyyar Barrister A.T. Shehu ya ce tun lokacin da gwamna Nyako ya soma mulkin jihar ta samu kudi fiye da nera miliyan dubu dari. Amma kuma babu wani aikin nera miliyan dubu daya da aka yi a jihar. Tambaya nan itace ina kudaden suka shiga ko me aka yi dasu? A. T. Shehu ya ce babu wani dalilin karbar wannan bashin.
To sai dai a nata martanin bangaren sabuwar PDP dake dasawa da gwamnan ta ce ba haka maganar take ba. Sakataren bangaren sabuwar PDP Mr. Peter Elisha ya ce ya cancanta kuma ya bi hanyar da ta dace na samo rancen. Ya ce ba su ne suka fara wannan irin abun ba. Gwamnatin tarayya ma tana rance. Sauran gwamnoni suna rance hatta wadanda aka fi basu kaso domin ana hako mai wurinsu. Ya ce babu wasu masana'antu a jihar sai dai ruwan da ake sarafawa ana sayarwa. Don haka jihar na bukatar rancen gina wasu abubuwa. Ya ce gwamna yana anfani da biliyoyi nera wurin biyan albashi da gyara makarantu da wasu ire-irensu. Idan ba da rancen ba ta yaya za'a gina masana'antu. Ya ce wannan rashin fahimmta ne.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.