A siyasar Amurka za'a yi zaben fidda gwani a birnin New York yau

'Yan takaran dake kan gaba, Trump na Republican da Clinton ta Democrats

A jiya ‘yan takarar neman Shugabancin Amurka sun nemi yardar jama’a game da daya daga cikin zaben mafi cin rai da za a yi a fidda gwanin yau Talata a birnin New York na nan Amurka.

Sanatan Vermont Bernie Sanders da ke biye da Hillary Clinton yayi wani taron nishadantarwa a wani wajen shakatawar da ake kallon zabga-zabgan gine-ginen birnin masu ban mamaki.

Kwana daya bayan da wasu gungun jama’a kimanin 28,000 suka fito gangamin neman zabensa a wani bangare na birnin. Kuri’un jin ra’ayi dai na nuna tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary na gaba da Sanders.

To amma shi kuma Bernie wanda ya bayyana kansa da dan siyasar Sassaucin ra’ayi mai halin ‘yan mazan jiya, ya fadawa gidan Talbijin na NBC cewa, a baya ma ya lashe zabe a jiyar da aka nuna an shiga gabansa a takarar neman shugabancin kasar.

Inda ya bayyana cewa, maganar gaskiya itace, kuri’ar jin ra’ayi ta yi musu raunin fahimtar tasirin nasarar da suke samu a siyasance a fafatawar da ake yi.

Shima Trump yana kan gaba a kintacen jin ra’ayin jama’ar akan abokan karawarsa Sanata Ted Cruz da gwamnan jihar Ohio John Kasich, to amma har yanzu ana ta hasashen ko wakilai nawa zai iya samu a jihar da cibiyar kasuwancin nasa take.