Magoya bayan Hamma Ahmadou wanda shi ne dankarar da hadakar jam'iyyun adawa suka tsayar ya kara da shugaban kasar a zaben zagaye na biyu da za'a yi ranar 20 ga wannan watan sun kalubali tsareshin da ake yi a kurkuku yayinda wadan ake zarginsu da laifi iri daya na waje suna walwala.
Magoya bayansa sun hakikance zamansa a kurkuku nada wani buri daban. Gwamnatin kasar nada wani burin siyasa ne da take son cimma.
Su 'yan adawa na jam'iyyar MODEN Lumana da na COPA sun sha alwashin tsayawa tsayin daka sai sun ga an maido da doka da oda a kasar ta Nijar. Sun ce Hamma dan takara ne da 'yan kasa suka bashi damar tsayawa.
Damar da 'yan kasa suka bashi na tsayawa zabe ya isa ta sa gwamnati ta sakoshi domin neman zaman lafiya. Magoya bayan Hamma Ahmadou sun zargi shugaban kasa mai ci yanzu wato Mahamadou Issoufou cewa shi ne baya son ya ga dan takarar a waje.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5