'Yan Takarar Da Suka Fusata Sun Sauya Sheka a Najeriya

Ginin Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya

kamar yadda 'yan siyasa su ka saba yi, a najeriya, 'yan takarar da su ke ganin ba a masu adalci ba, na ta canza sheka daga wannan jam'iyyar zuwa waccan.

Bisa ga dukkan alamu kananan jam’iyu a Najeriya sun soma samun tagomashi a wannan karon ganin yadda mafusatan 'ya'yan manyan jam’iyu a Najeriya irinsu APC da PDP ke rige-rigen komawa wasu sabbin jam’iyu domin hakarsu ta cimma ruwa, kuma wannan ma ko na zuwa ne yayin da yawan jam’iyyu a kasar ke tasamma 91.

Na baya bayan nan shine irin yadda wasu manyan yan siyasa a jihohin Adamawa da Taraba suka sauya sheka zuwa irin wadannan sabbin jam’iyun domin tsayawa takara.

Dr Daniel Shaga Ismail,wani tsohon dan siyasa a Adamawa da kuma ya sha takarar kujerar gwamna, ya bayyana dalilansa na komawa daya daga cikin irin wadannan sabbin jam’iyun, wato sabuwar jam’iyyar All Blending Party (ABP.).

Shima wani dan takarar a inuwar Social Democratic Party, SDP,Chief Emmanuel Bello, ya ce sun kimtsa tsaf domin fuskantar manyan jam’iyun.

Ga wakilinmu Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Fusatattun 'Yan Takara Daga Manyan Jam’iyu Irisnu APC da PDP, Na Cigaba Da Sauya Sheka