Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Sojin Najeriya Sunyi Nasara Kan 'Yan-Ta'adda Na Boko Haram


Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai
Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai

Dakarun sojin Najeriya sun fafutuki 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram, da safiyar yau Alhamis.

A jiya ne mayakan Boko Haram sukai yunkurin kai hari a sansanin sojojin Najeriya, dake Katarko a karamar hukumar Gujba dake jihar Yobe, al'amarin da ya haddasa fargaba a zukatan jama'ar jihar.

Shelkwatar sojin kasa a Abuja, ta fidda sanarwa inda tace dakarunta na bataliya ta 120, dake karkashin rundunar Operation Lafiya Dole dake yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas sun fafutukesu.

Kakakin shelkwatar sojojin kasar Birgediya Janaral Texas Chukwu, cikin wata sanarwa da ya fitar dazu-dazunnan, ya ce mayakan na Boko Haram sun gamu da fushin dakarun sojin kasar, da suka koresu suka ranta a na kare, kana aka bisu cikin dajin don kamo su.

Yazuwa yanzu sojojin sun maido da kwanciyar hankali da lumana a yankin, harma an shiga sassaita al'amura, don haka ana kira ga jama'ar jihar Yobe, dasu ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, sai dai sanarwar batace komi kan hasarar da aka samu a bangarorin biyu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:29 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG