Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tsofaffin Sojin Najeriya Sun Gudanar Da Taro


Tsofaffin sojojin Najeriya sun gudanar da wani taron karawa juna sani, don kyautata dangantakar su da fararen hula.

Kungiyar tsofofin sojin Najeriya ta gudanar da taron karfafa gwiwa ga mambobinta, ta yadda zasu yi rayuwa mai ma’ana da samun karbuwa a tsakanin al’umma, don bada tasu gudunmmawar wajen ci gaban kasa.

Taron wanda ya tattaro kan shuwagabanni da magatakardan kungiyar daga jihohi talatin da shida da birnin tarayya Abuja, sun sami karuwa kan yadda zasu inganta ma’amalarsu da fararen hula da naman hanyoyin dogaro da kansu.

Manjo Gabriel Ad’ofikwu wanda ya wakilci shugaban kungiyar tsofofin sojojin na kasa, Birgediya Janar Adakole Jones Akpa, ya fara ne da cewa kowa nada hakkin kula da tsofofin sojojin.

Wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka, Zainab Babaji ta aiko muna a wannan rahoton daga jihar Plateau.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG