Masana tattalin arziki a Najeriya na nuna fargaba kan yadda karin albashi zai shafi farashin kayayyaki a kasar.
A ranar Talatar da ta gabata, hadakar kungiyoyin kwadago da gwamnati suka amince da karin albashi mafi karanci daga dubu N18 zuwa N30.
“Tun da ya shafi ma’aikata na gwamnati da na kamfanoni, su kamfanoni akan abubuwan da suke yi ne sukan kara farashin kayayyakinsu domin s samu kudaden da za su karawa ma’aikatansu.” Inji masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu.
Ya kara da cewa, a matsayinsu na masana a fannin tattalin arziki, Aliyu ya ce “amma kuma ba zai yi wu a hana karin ba, domin doka ce ta ce a yi shi.”
Aliyu ya kuma ce lokaci da ya kamata a yi karin albashi ba a samu damar yin hakan ba, wanda a lokacin ne ‘yan Najeriya suka fi bukatars shi.
“Idan ka duba hauhawan farashin da ya shigowa tattalin arziki na shekara hudu da suka wuce tun 2015 lokacin da ya kamata a yi karin albashin ba a yi ba.”
Saurari cikakkiyar hirar da wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya ya yi da masanin tattalin arziki Malam Yusha'u Aliyu:
Facebook Forum