Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Hari Kan Wasu Matafiya a Borno


Sojojin Operation Lafiya Dole sun ceto wata tsohuwa da jikarta daga wani sansanin 'yan Boko Haram.
Sojojin Operation Lafiya Dole sun ceto wata tsohuwa da jikarta daga wani sansanin 'yan Boko Haram.

Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun bude wuta akan motocin wasu matafiya sannan suka kona dogayen motoci da ke dauke da kayan abinci, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun kai wa wasu matafiya harin kwantan-bauna a babbar hanyar jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata, a cewar jaridar Daily Trust.

Jaridar ta ruwaito wani sojin sa-kai da aka fi sani da “Civilian JTF” wanda ya ce an kai wa matafiyan hari ne a tsakanin yankin da ake kira Longomani da Musini a kusa da garin Ngala da misalin karfe 5:30 na yamman jiya Alhamis.

Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun bude wuta akan motocin wasu matafiya sannan suka kona dogayen motoci da ke dauke da kayan abinci, kamar yadda majiyar ta Civilian JTF ta fadawa jaridar Daily Trust ta wayar talho.

A cewar majiyar, da yawa daga cikin fasinjojin sun mutu sannan wasu da dama sun arce cikin daji domin neman mafaka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG