Malaman addinin musulunci fiye da 200 tare da sauran al’ummar yankin arewa maso gabashin Najeriya da ke da zama a kudu maso yammacin Najeriya musamman ma Lagos, sun gudanar da taron addu’o’i na samun zaman lafiya a yankinsu na Arewa da kuma kasa baki daya,musanman kan rikicin yan Boko haram.
Alhaji Muhammed Mustapha, wanda shi ne Mai Kanuri-Be na birnin Lagos, shi ne ya jagoranci addu’ar. Kuma bayan taron addu’ar ya gaya ma wakilinmu a Lagos Babangida Jibrin cewa sun yanke shawarar yin addu’ar ce saboda har yanzu Boko Haram na hallaka mutane tare da kwace masu shanu da dauran dukiyoyi.
Daga cikin wadanda su ka halarci taron addu’ar har da wadanda su ka gudo daga arewa maso gabashin Najeriya kamar irinsu Shattima Alhaji Abba wanda ya nuna godiya kan yadda ake kulawa da su ‘yan gudun hijirar.
Your browser doesn’t support HTML5