An Karrama Davido A Amurka

Davido

Shi dai Davido haifaffen birnin Georgia ne da ke  jihar Atlanta da ke Amurka wanda hakan ke nufin shi Ba’amurke ne kuma dan Najeriya.

Majalisar Dokokin Gerogia da ke Amurka ta karrama mawakin Afrobeat na Najeriya David Adeleke da aka fi sani da Davido.

Majalisar ta karrama mawakin da matsayin “Fitaccen Dan Georgia.”

Shi dai Davido haifaffen birnin Georgia ne da ke jihar Atlanta da ke Amurka wanda hakan ke nufin shi Ba’amurke ne kuma dan Najeriya.

“Da safen nan na je zaman Majalisar Dokokin Georgia inda na hadu da Wakilai a Majalisar da Sanatoci a jihar, inda aka karrama ni da matsayin ‘Fitaccen Dan Georgia” Dadvido ya rubuta a shafinsa na Instagram a ranar Juma’a.

A lokacin rubuta wannan labari, mutum sama da dubu 383 ne suka danna alamar kaunar wannan bayani da Davido ya wallafa a shafinsa, sa’a shida bayan da ya saka.