A Karon Farko Gwamntin Jihar Borno Ta Nada Makaho a Matsayin Mai Bai Wa Gwamna Shawara

  • Ibrahim Garba

Wani makaho da sandarsa.

A wani yinkuri na kyautata ma miskinai a jihar Borno, a karon farko gwamanatin jihar ta nada wani miskini a babban matsayi.
Gwamnatin jihar Borno ta nada Sarkin Makafin Jihar Alhaji Bukar Mai Abacha a matsayin babban mai bai wa gwamnan jihar shawara kan miskinai.

Da ya ke jawabi a wurin bayar da tallafin Dangote a Gidan Gwamnatin Jihar, Sarkin Makafin ya ce daukakar da gwamna Kashim Shattima ya ba shi ba tasa kadai ba ce. Daukakar ta shafi duk wani miskini a jihar.

Wakilinmu a jihar Borno Haruna Dauda Biu ya ruwaito shugabar bankin masu kananan masana'antu ko "micro-fimnace bank" Hajiya Zainab Umar Kolo na cewa 'yan borno mabukata wajen 54,000 ne za su amfana da kudin da Gidauniyar Dangote za ta raba wajen Naira miliyan dari biyar da arba'in ta yadda kowane miskinin da ya cancanta zai sami Naira dubu goma.

Your browser doesn’t support HTML5

Nada Miskini