A cikin kasidar da ya bayar Injiniya Adama Nambre daga Ghana ya ce kimanin mutane biliyan daya ne basu da ruwan sha a duniya yawanci suna a nahyar Afirka suke. Haka ma mutane biliyan biyu basu da wutar lantarki a duk fadin duniya. Yawancinsu suna nahiyar Afirka ne.Nanda shekarar 2030 fiye da kashi 60 na al'ummar Afirka zasu shiga matsalar karancin muhali. Canjin yanayi zai kai ga karancin ruwan sha wanda zai kaiga asarar muhalli domin lamarin zai shafi harkokin noma da kiwo.
Injiniya din ya bayar da shawar komawa ga samun makamshi ta hanyar rana domin a rage sare itatuwa ana girki da su.
Shugaban kungiyar injiniyoyin Najeriya Mustapha Balarabe Shehu ya ce inda gwamnatin Najeriya zata ba kungiyar hadin kai da ta kawar da barazanar. Ya ce shugabannin Najeriya su yadda cewa injiniyoyin Nageriya zasu iya yin aikin sabo da sai ana da imani a kan mutum za'a ce ya yi abu. Idan an ba mutum abun da bai iya yi ba yana iya jawo wani su yi tare. Ta haka ne a ke bunkasa masana'antu a kuma habbaka tattalin arziki. Abun da yake son gani shi ne gwamnati ta amince masu. Wuraren da kuma suke kuskure a fada masu su gyara. Idan aka amince masu aka basu ayyukan da yakamata su yi kasar zata bunkasa gaba daya.
Kwamishana daga arewa maso gabas dake fuskantar kalubalen tsaro Injiniya Shehu Hadi Ahmed ya ce ya zama wajibi a dauki kwararan matakai wajen tantance ijiniyoyin dan kawar da bara gurbi da kan yi aikin da bashi da inganci.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da rahoto.