'Yansanda a jihar sun gano wasu gungun 'yan luadi da 'yan madigo ciki har da wasu manyan mata da maza da suke yaudarar kananan yara suna lalata da su. Wata ta ce hankalinsu a matsayinsu na iyaye a jihar ya tashi domin fyade da ake yiwa 'ya'yansu da yin madigo da luadi da su. Wani kuma ya ce abun abu ne na tashin hankali.
Masu yin lalatar da yaran sukan fake ne da yin anfani da kudi ko kuma kayan alatu domin cimma muguwar aniyarsu. Tuni rundunar 'yansandan jihar ta cafke wasu cikin masu lalata da yaran. Wadanda suka gudu kuma ana nemansu ruwa a jallo.
Kakakin 'yansandar jihar DSP Muhammed Ibrahim ya tabbatar da lamarin. 'Yansandan har ma sun gurfanar da wasu da suka kama gaban shari'a cikinsu har da wani mai shekaru saba'in da hudu da haihuwa. Wannan dattijon najadun yana luadi da yara hudu masu shekaru kasa da goma sha biyar. DSP Ibrahim ya ce lamarin abun takaici ne don haka 'yansanda na son hadin kan jama'a. Ya roki mutane da su basu rahoton du wadanda suka gani suna irin wannan aika-aikar domin a yi maganinsu.
Ita ma kungiyar kare hakin 'yan Adamawa tana kan gaba wajen yaki da ire-iern masu aikata wannan muguwar dabi'a. Onarebu Huseini Gambo shi ne shugaban kungiyar kuma ya ce abun da suke so shi ne su wayar da kan jama'a kana suna bin sawun shari'a su tabbatar an aikata gaskiya. Suna son su tabbatar an yi hukuncin da ya kamata kada a dauki wata hanya daban.
Masana halayyar dan adam irin su Malam Yakubu Musa Uba sun ce son mulki da son kudancewa da wuri da rashin tsoron Allah suna cikin dalilan da suka sa wasu suna irin wannan aika-aikar, wato fadawa cikin yin luadi da madigo ko yin fyade. Ya shawarci iyaye su rika kula da 'ya'yansu su kuma rika jan kunnuwan 'ya'yansu. Su kuma hukumomi ya gargadesu su yi hukunci mai tsanani. Duk wanda aka kama a yi masa hukunci mai tsanani ko da ma ta kama a yi hukuncin kisa. Hukuncin wata shida a gidan kaso ko shekara biyu ko tarar nera dubu hamsin ke dada karfafa masu ta'asar su cigaba da yi.
Ga Ibrahim Abduaziz da rahoto.