ABUJA, NIGERIA - Ministan ya ce duk labaran da ake yadawa a wasu kafafen yada labarai ba su da tushe balle makama domin har yanzu ana bai wa ‘yan kasar takardar izinin shiga kasar hadaddiyar daular larabawa UAE.
“A hukamance ba a sanar da mu cewa an daina bai wa ‘yan Najeriya visar zuwa kasar UAE ba. Na ga labarin na kira Ambasadan kasar ya bayyana min cewa shi ma kansa bai san da wannan labari ba, domin babu wani umarnin daina bada visa ga ‘yan Najeriya da aka turo masa, ya fada min cewa ko shekaran jiya sai da suka ba wa 'yan Najeriya visa.”
Ambasada Dada ya kara da jaddada cewa “abin da ya kamata ‘yan Najeriya su sani shi ne, kowace kasa na da hurumin ko ta bada izinin shiga ko ta hana, ana iya bai wa mutum visa kuma ya je ya sauka a airport a hana shi shiga kamar yadda muma Najeriya muna iya hana mutum ya shigo ko da an ba shi visa yana zuwa nan filin jiragen sama na Abuja, jami’an kula da shige da fice su hana mutum saboda watakila suna da wani bayanan sirri.”
Kan batun zargin nuna halin ko’inkula da gwamnatin Najeriya ke yi ministan ya ce kasar bata taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare muradin ‘yan Najeriya da Najeriya a kasar waje.
Ya ce “Muna iya bakin kokarin mu domin a dukkan ofisoshin jakadancin da muke da su guda dari da hudu (104) babban abinda muka fi maida hankali a kai da kuma fada wa jami’an mu shine kare mutuncin ‘yan Najeriya. Amma abun bakin cikin shi ne yadda wasu ‘yan kalilan ke yin wasu dabi’u da basu kamata ba, wasu na tafiya ba tare da takardu ba, wasu kuma visa ta kare amma su ki dawowa, da dai sauransu.”
Kan batun dawo da wasu 'yan Najeriya sama da dari biyar da aka yi, Ambasada Dada ya bayyana cewa sun saba wa dokokin kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa ne inda ya bada misalin yadda wasu ke sana’ar kasuwanci, wasu sayar da giya da kwayoyi, wanda hakan ya saba wa dokokin kasar.
Saurari yadda hirar tasu ta kaya da wakilin Muryar Amurka Al-Hassan Bala:
Your browser doesn’t support HTML5