A wurin bikin gwamna Shettima da 'yanuwansa da abokan arziki suka dauki nayin wasu marayu hamsin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kashe masu iyaye.
Bikin shi ne karon farko da gwamnan yayi bikin cika shekara tunda ya hau karagar mulki shekaru biyar da suka gabata.
Bikin ya samu halartar 'yanuwa da abokanan arziki dake cikin jihar da ma wajen jihar da suka hada da tsohon gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ma a can baya, ya dauki dawainiyar karatun wasu marayun da Boko Haram ta kashe masu iyaye daga jihar Borno.
Bankin Zennith ma ya dauki dawainiyar karatun wasu marayun guda hamsin nan da shekaru tara masu zuwa. Bankin ya bada takardar kudi amma ba'a bayyana ko nawa ba ne.
Gwamnan ya nuna jin dadinsa game da karramawa da aka yi masa amma ya nuna bacin ransa da wasu furuci da yace maigdansa Sanata Modu Sheriff na yi a kansa. Gwamna Shettima ya yi kwamishanan ma'aikatu biyar lokacin da shi Modu Sheriff ke gwamnan jihar.
Gwamna Kashim Shettima yace shi bai taba neman tashin hankali da Modu Sheriff ba, amma Ali Sheriff ne ke neman tashin hankali da shi.
Yace yayi duk iyakacin kokarinsa domin su zauna lafiya. Yace shi ba zai taba zagin Ali Modu Sheriff ba duk da yana kiran shi gwamnan karamin yaro. Yace amma yau ga karamin yaro ya cika shekara hamsin.
Gwamnan na Borno yace duk lokacin da wani dan Adama ya nuna cewa shi ma karamin allah ne a lokacin ne Allah ke kaskantar da mutum.
Ga rahoton Haruna Dauda domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5