Saboda wannan garambawul da aka yi ya sa Muryar Amurka ta zanta da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ali Ndime wanda yake wakiltar kudancin Borno.
An fara tanbayarsa ko wannan garambawul da suka yi ke nan bangarorin majalisar biyu wato wasu dake kiran kansu "Like Minds" da "Unity Forum" yanzu sun zama daya ke nan sai Sanata Ali Ndime yace abun da ya faru ke nan. Yace ai dama can siyasa kare muradu ne. Dama can abun da ya kawo kalubale saboda muradun ne da basu zo daya ba. Mutane suna neman a biya masu bukatunsu shi ya sa tafiya bata tafi daidai ba. Ganin an kasa cigaba ya sa aka duba a gano abun da zai sa a cigaba sai aka yanke shawara a yiwa tsarin kwamitoci garambawul domin a karawa wasu kwamitoci.
Sanata Ali Ndime yace bayan shekara daya ana cecekuce yanzu yakmata su tsaya su yi aiki tare, su mance abun da ya faru can baya, su nemi cigaba domin 'yan Najeriya suna jira a yi masu aiki.
Bayan an yi garambawul din su 'yan jam'iyyar APC dake majalisar sun zauna sun yi shawara cewa yanzu fa basu da wani korafi akan yadda aka raba kwamitoci saboda haka yakamata su manta da baya su dukufa da yin aiki domin 'yan Najeriya su gani a kasa.
To saidai har yanzu suna da matsala daya kasancewa mataimakin shugaban majalisar ba dan jam'iyyarsu ba ne. Har yanzu suna fada akan wannan lamari dake ci masu tuwo amkwarya.
Ga karin bayani.