Masu ikirarin jihadi sun hallaka akalla manoma 40 a jihar Borno da ke shiyar arewa maso gabashin Najeriya a jerin tashe-tashen hankulan da suka afkawa yankin mai fama da rikici, kamar yadda wani jami'in gwamnati ya bayyana a yau Litinin.
Da yammacin jiya Lahadi, mayakan kungiyar Iswap suka yi dimbin manoma kofar rago a garin Dumba dake gabar tafkin Chadi tare da harbesu har lahira, kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar Borno, Usman Tar, ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Rahotann farko sun bayyana cewar an hallaka manoma 40 sannan ana neman inda wasu da dama suka shiga domin sake hadasu da iyalansu," a cewar Tar .
Gwamnatin jihar ta ba da umarnin dakarun da ke yaki da masu ikirarin jihadin su bi sawu tare kawo karshen masu tada kayar bayan dake gudanar da harkokinsu a kewayen garin Dumba da maboyarsu a fadin yankin tafkin Chadi, a Cewar Tar.
Manoman sun zarta iyakar da dakarun suka shata musu domin yin noma da kamun kifi a yankin da ya zama mafaka ga mayakan ISWAP da abokan hamayyarsu na Boko Haram da nakiyoyin da aka birne da kuma yiyuwar kai hare-hare cikin dare," a cewar kwamishinan.