Jami’an Falasdinu sun ce mutum shida sun jikkata a wani harin Isra’ila na jirage marasa matuka a wani asibiti a arewacin Gaza inda ake yiwa yara rigakafin cutar polio, galibin su yara. Sojojin Isra’ila sun musa kai wannan harin.
A ranar Asabar aka kai harin a arewacin Gaza, inda dakarun Isra’ila sukayiwa kawanya sannan aka kauracewa yakin a shekarar da ta gabata. Isra’ila tayi ta kai sabbin hare hare cikin ‘yan makonnin da suka gabata wanda ya kashe daruruwan mutane sannan ya raba mutane da dama da matsugunan su.
An kasa tantance gaskiya akan bayanan farmakin masu cin karo da juna. Dakarun Isra’ila sun yi ta harin asibitoci tsawon lokacin da aka kwashe ana yakin, inda suka ce mayakan Hamas suna amfani da su don gudanar da ayyukan kungiyar, zargin da jami’an lafiyar Falasdinu suka musa.
Hukumar Lafiya ta duniya WHO da hukumar MDD mai bibiyar al’amuran yara wato UNICEF, da sukayi hadin gwiwa a gangamin rigakafin cutar ta Polio sun bayyana damuwa akan harin.
inda mai magana da yawun UNICE Sosalia Bollen ta ce "samun labarin harin na da tashin hankali, kasancewar asibitin Sheikh Radwan ya kasance daga cikin asibitocin da iyaye suke iya kai yaran su ayi musu rigakafi."