Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Harajin VAT Kan Man Dizil, Iskar Gas

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bullo da sabbin dabarun jan hankalin masu zuba jari a bangaren mai da iskar gas din kasar.

Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Kasar, Wale Edun ne ya bayyana dabarun jan hankalin 2, a sanarwar da ya fitar a jiya Laraba.

A cewar sanarwar da ma’aikatar kudin ta fitar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Muhammad Manga yace manufar dabarun sune sake farfado da bangaren mai da iskar gas din Najeriya.

Ta kara da sanar da cewa daga yanzu ba za a bukaci biyan harajin cinikayya (VAT) a kan shigo da muhimman albarkatun makamashi ko kayayyaki ba.