Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin babbar jojin Kano Mai Shari’a Dije Aboki ta dage yanke hukunci a kan bukatar dakatar da sarkin kano na 15, Aminu Ado Bayero, ci gaba da aikin gudanar da gyare-gyare a karamar fadar Nasarawa mai tsahon tarihi.
Mai Shari’a Aboki ta tsayar da ranar 10 ga watan Oktoba domin yin hukunci a kan bukatar, ta kuma bada umarnin like dukkanin shari’o’in dake da nasaba da wannan a alon fidda bayanan kotun domin tabbatar da cewa an sanar da dukkanin bangarorin dake cikin shari’ar game da halin da ake ciki.
Masu kara, da suka hada da gwamnatin jihar kano da antoni janar na jihar da majalisar masarautar Kano, sun bukaci a bar fadar a yadda take domin adana tarihi da al’adu, inda suke turjiya akan zamanantar da ita.
Sunan sarki aminu ado bayero ne kadai a cikin kunshin wadanda ake kara.
Dandalin Mu Tattauna