Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsaurara Tsaro A Ribas Saboda Zanga-Zangar Mambobin PDP Kan Zaben Kananan Hukumomi


Rivers PDP
Rivers PDP

Yawan masu zanga-zangar ya janyo cunkoson ababen hawa a kan tituna.

Mambobin jam’iyyar PDP sun gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin hukumar tsaron farin kaya (DSS) da fadar gwamnatin jihar Ribas dake birnin Fatakwal.

An jibge dimbin jami’an tsaro yayin da dandazon masu zanga-zangar suka fara taruwa a sakatariyar PDP ta jihar.

Yawan masu zanga-zangar ya janyo cunkoson ababen hawa a kan tituna.

Daga bisani an ga masu zanga-zangar suna daga kwalaye, tare da rera wakokin gwagwarmaya sannan suka rika guje-guje akan manyan hanyoyi.

Masu zanga-zangar da suka taso daga sakatariyar pdp dake kan titin zuwa aba na birnin fatakwal, zun zarce zuwa ofishin dss dake tsohuwar gra inda suka mika korafinsu daga nan suka zarce zuwa fadar gwamnatin jihar.

Sun samu rakiyar mambobin jam’iyyar APC tsagin Tony Okocha a yayin gangamin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG