Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Bada Shawarar Mayar Da Mulkin Najeriya Na Karba-Karba


Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Hoto: Facebook/Atiku Abubakar)

A wasikar daya aikewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, wanda ya kasance shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, Atiku ya bukaci majalisun tarayyar Najeriya su yi nazarin shawarar tasa a aikin gyaran kundin tsarin mulkin da suke yi.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bada shawarar mayar da mulkin Najeriya na karba-karba tsakanin yankunan kudanci da arewacin najeriya kuma mai wa’adin shekaru 6 falan daya.

A wasikar daya aikewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, wanda ya kasance shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, Atiku ya bukaci majalisun tarayyar Najeriya suyi nazarin shawarar tasa a aikin gyaran kundin tsarin mulkin da suke yi.

Wasikar wacce ke dauke da kwanan wata 29 ga watan agustan daya gabata, na kuma dauke da sa hannun atikun.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci a kara sakin layi “a” kan sashe na 130 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da zai kasance kamar haka: “za’a rika karba-karba akan mukamin shugaban kasa tsakanin yankunan mulkin tarayyar kasar nan guda 6 a bisa tsarin zango daya na shekaru 6 da zai rika kadawa daga yankin arewaci zuwa kudu duk bayan shekaru 6 nan ma.”

Ya kuma bukaci a gyara sashe na 135 (2) ya kasance kamar haka: “a bisa la’akari da tanade-tanaden karamin sashe na 1, shugaban kasa zai bar mukaminsa bayan karewar wa’adin mulkinsa na shekaru 6 farawa daga ranar da aka zabe kan wannan mukami.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG