Kotu Ta Yanke Hukuncin Dauri Ga Wanda Ya Nuna Wa Vinicius Da Chukwueze Wariya

  • VOA Hausa

Samuel Chukwueze da Vinicius Junior

An yankewa wani magoyin bayan kungiyar kwallon kafa ta Mallorca da furta kalaman wariya ga tauraron kungiyar Real Madrid Vinicius Junior da tsohon dan wasan Villarreal Samuel Chukwueze daurin shekara guda a gidan kaso tare da haramta masa shiga filayen wasan kwallon kafa tsawon shekaru 3 a yau Alhamis.

An samu masoyin kwallon kafar da laifuffuka 2 da suka sabawa tarbiya da mutuntaka, kuma kasancewar ya aikata haka ne da niyar nuna wariyar launin fata ya kara ta’azzara lamarin, a cewar sanarwar da kungiyar Real Madrid ta fitar.

Cin zarafin Vinicius ya faru ne lokacin da kungiyar Real Madrid ta lallasa Mallorca da ci 1 mai ban haushi a filin wasa na Son Moix a watan Febrairun 2023, kafin daga bisani wannan magoyin bayan ya ci zarafin Chukwueze, wannan karon a filin wasan AC Milan, makonni 2 tsakani.

A cewar kungiyar Real Madrid, an dakatar da hukuncin daurin “bayan da wanda ake tuhumar ya nemi gafara tare da nuna nadama, inda ya aike da wasika ga Vinicius, bayan da ya kammala samun horo akan daidaiton jinsunan bil adama da kyamar wariya.”