‘Yar wasan Najeriya Folashade Oluwafemiayo ta doke tarihin da ta kafa a wasan daga nauyi ta mata a wasannin nakasassu na Paralympics da aka kammala a Paris.
Oluwafemiayo ita take rike da zinaren daga nauyi ajin kilo 86.
Sai ga shi ta shafe wannan tarihi inda ta kafa sabo tarihi wajen daga nauyin kilo 167 a gasar ta nakasassu.
Deng Xuemei ta kasar China ce ta lashe kyautar azurfa inda ta daga nauyin kilo 155 sai Nadia Ali ‘yar kasar Masar da ta lashe kyautar tagulla bayan da ta daga nauyin kilo 145.
A ranar Lahadi aka kammala gasar ta Paralympics inda aka yi wasanni wuta a bikin rufe gasar.
Nasarar ta Oluwafemiayo na zuwa ne yayin da ‘yan wasan Super Eagles na Najeriya suka samu nasara akan ‘yan wasan Jamhuriyar Benin da ci 3-0 a wasan neman gurbin shiga gasar nahiyar Afirka ta AFCON.
Dandalin Mu Tattauna